Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta dakatar da wasu fitattun jaruman Kannywood biyu, Adam Garba da Amina Uba Hassan

Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta dakatar da wasu fitattun jaruman Kannywood biyu, Adam Garba da Amina Uba Hassan,

Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta dakatar da wasu fitattun jaruman Kannywood biyu, Adam Garba da Amina Uba Hassan, daga gudanar da harkokin fim a faɗin jihar na tsawon shekara guda.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Comrade Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a madadin shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, an bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan bayyanar jaruman a wani bidiyo da hukumar ta ce ya saɓa wa tarbiyya da ƙa’idojin masana’antar Kannywood.

Sanarwar ta ce bidiyon ya jawo muhawara da ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar Jihar Kano, lamarin da ya sa hukumar ta ɗauki matakin ladabtarwa domin kare mutunci da martabar masana’antar fim ta Kannywood.

Hukumar ta kuma bayyana cewa dokokinta sun ba ta ikon hukunta duk wani ɗan masana’antar fim da ya karya ƙa’idojin da aka shimfiɗa, tare da gargadin cewa rashin bin umarnin dakatarwar na iya jawo ƙarin hukunci mai tsauri.

Shugaban hukumar, Malam Abba El-Mustapha, ya yi kira ga masu harkar Kannywood da su guji duk wani aiki da ka iya zubar da mutuncinsu ko rage darajar masana’antar a idanun jama’a.

Haka kuma, ya umarci masu shirya fina-finai da daraktoci da su mutunta umarnin dakatarwar, yana mai cewa duk wanda aka samu yana aiki da jaruman da aka dakatar zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

0 $type={blogger}: