Kotu ta bayar da belin N100m ga El-Rufai kan zargin yin kutse a wayar Nuhu Ribadu.

Kotu ta bayar da belin N100m ga El-Rufai kan zargin yin kutse a wayar Nuhu Ribadu.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin naira miliyan 100 ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin yin kutse ba bisa ka’ida ba kan tattaunawar wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta bayar da belin a ranar Litinin tare da sharadin cewa El-Rufai zai gabatar da wanda zai tsaya masa wanda dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnatin tarayya mai matsayi na Grade Level 17 ko sama da haka.

Kotun ta kuma ce wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance yana zaune a yankin Maitama ko Asokoro da ke Abuja, sannan ya gabatar da takardar mallakar gida mai darajar da ba ta gaza kudin belin ba.

Haka kuma, kotun ta umurci El-Rufai da ya mika fasfonsa na kasa da kasa tare da neman izinin kotu kafin ya fita daga Najeriya.

Mai shari’ar ta kuma umurce shi da ya rika zuwa hedkwatar DSS a kowace Juma’ar karshen wata domin sanya hannu har sai an kammala shari’ar.

Hukumar DSS na tuhumar tsohon gwamnan da laifuka guda biyar da suka shafi zargin kutse cikin sadarwar wayar NSA.

A cewar DSS, El-Rufai ya yi wasu kalamai yayin wata hira da gidan talabijin wadanda suka nuna cewa yana da masaniya kan mutanen da suka yi kutse cikin wayar Ribadu.

Sai dai El-Rufai ya musanta aikata wani laifi, yana mai cewa kalaman da ya yi yayin hirar talabijin ba furuci bane na amsa laifi.

0 $type={blogger}: