Adadin Wadanda Suka Mutu a Lebanon Ya Karu Bayan Sabbin Hare-haren Israi'la.

Adadin Wadanda Suka Mutu a Lebanon Ya Karu Bayan Sabbin Hare-haren Israi'la.

Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon sabbin hare-haren sama da Isra’ila ta kai a sassa daban-daban na ƙasar Lebanon, duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka ta jagoranta wadda aka ƙara wa’adinta tsakanin Isra’ila da kungiyar Hezbollah.

Hare-haren sun afku a yankunan kudanci da gabashin Lebanon, ciki har da gundumar Baalbek, inda wani hari da aka kai kan ginin gidaje ya kashe wani babban jami’in kungiyar Palestinian Islamic Jihad tare da ‘yarsa mai shekara 17.

Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce sabbin hare-haren sun sa adadin wadanda suka mutu tun bayan fara hare-haren Isra’ila a watan Maris ya haura mutane 3,200, yayin da dubban mutane suka jikkata.

Sabbin rikice-rikicen sun faru ne kwanaki kadan bayan jami’an Lebanon da Isra’ila sun gudanar da tattaunawa a birnin Washington, inda suka amince da tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki 45.

Isra’ila ta ce sojojinta sun kai hare-hare kan wuraren da suke zargin na kungiyar Hezbollah ne, ciki har da wuraren ajiye makamai da sansanonin gudanar da hare-hare.

A nata bangaren, Hezbollah ta ce ta kai hare-haren jiragen yaki marasa matuka da makamai masu linzami kan wuraren sojin Isra’ila a kudancin Lebanon domin mayar da martani.

An kuma umarci mazauna wasu kauyuka da garuruwa su fice daga gidajensu kafin hare-haren, lamarin da ya kara jefa mutane cikin matsanancin halin gudun hijira. Kungiyoyin agaji sun ce fiye da mutane miliyan daya sun rasa matsugunansu sakamakon rikicin da ke ci gaba.

0 $type={blogger}: