Tinubu Ya Ba da Umarnin Ceto Wadanda Aka Sace a jihar Oyo Bayan Kisan Malami Daya.

Tinubu Ya Ba da Umarnin Ceto Wadanda Aka Sace a jihar Oyo Bayan Kisan Malami Daya.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan daya daga cikin malaman makarantar da aka sace a harin da ‘yan bindiga suka kai a jihar Oyo, inda ya bayyana lamarin a matsayin “ta’addanci da rashin tausayi”.

A wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, an ce ‘yan bindiga sun kai hari makarantu da ke yankin Esiele a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo, inda suka sace malamai da dalibai da yara kanana daga makarantu daban-daban.

Tinubu ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kara kaimi wajen gudanar da aikin ceto domin kubutar da sauran wadanda aka sace tare da kamo masu hannu a harin.

Shugaban ya kuma jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya shafa tare da yabawa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, bisa matakan da yake dauka domin magance matsalar.

Ya ce Sufeto Janar na ‘yan sanda na jagorantar aikin kai tsaye tare da amfani da fasahar zamani da bayanan sirri wajen neman maharan, yana mai cewa ana sa ran samun gagarumar nasara nan ba da jimawa ba.

Tinubu ya sake kira da a kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai cewa yawaitar sace-sacen mutane da matsalar tsaro a Najeriya na nuna bukatar samar da karin tsaro a matakin jihohi.

0 $type={blogger}: