Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kwara ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun sace mutane 10 daga fadar sarkin Yashikira da ke karamar hukumar Baruten a jihar.
A cewar sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Adetoun Ejire-Adeyemi, ta fitar a ranar Litinin, harin ya kuma shafi ofishin ‘yan sanda ta Yashikira a lokaci guda da misalin karfe 2:00 na dare.
Sanarwar ta bayyana cewa maharan dauke da makamai sun kai harin hadin gwiwa kan ofishin ‘yan sanda da kuma fadar sarkin a lokaci guda.
“Wadannan miyagun mutane sun kai harin da misalin karfe 2:00 na dare, inda suka farmaki hedikwatar ‘yan sanda da kuma fadar sarkin na Yashikira a lokaci guda,” in ji sanarwar.
A yayin harin, an kona wani bangare na fadar sarkin, sannan aka sace mutane 10 aka tafi da su zuwa wurin da ba a sani ba. Sai dai ‘yan sanda sun samu nasarar dakile harin da aka kai ofishin su.
Bayan lamarin, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ojo Adekimi, ya bayar da umarnin fara wani gagarumin aikin leken asiri da hadin gwiwa da sojoji da jami’an sintiri na daji da kuma ‘yan banga domin bin sahun maharan da kuma ceto wadanda aka sace.
Ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar ‘yan sanda ba za ta bari ‘yan ta’adda su tayar da hankalin jama’a ba, yana mai cewa za a dauki dukkan matakan da suka dace domin murkushe su.
An kuma kara tsaurara matakan tsaro a yankin Yashikira da sauran sassan karamar hukumar Kaiama, tare da ci gaba da bincike da sintiri a dazuka.
Wannan sabon hari na zuwa ne bayan wani harin da aka kai a jihar Kwara wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku tare da sace wasu masu ibada a lokacin daren addu’a a wani cocin da ke yankin Ekiti na jihar.

0 $type={blogger}:
Post a Comment