NEMA ta dawo da ‘yan Najeriya 497 daga Jamhuriyar Nijar cikin shirin komawa gida bisa radin kai

NEMA ta dawo da ‘yan Najeriya 497 daga Jamhuriyar Nijar cikin shirin komawa gida bisa radin kai

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta dawo da ‘yan Najeriya 497 daga birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar zuwa Kano a wani shiri na komawar ‘yan ƙaura gida bisa radin kai.

An karɓi waɗanda suka dawo a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano ranar Juma’a da misalin ƙarfe 12:40 na rana, kamar yadda jami’ai suka tabbatar.

Shugaban Ayyuka na ofishin NEMA a Kano, Dakta Nura Abdullahi, ya ce wannan ba korar tilas ba ce, sai dai komawa gida cikin yardar kansu tare da tallafin gwamnatin tarayya ta ma’aikatar harkokin waje.

Ya bayyana cewa an gudanar da aikin tare da haɗin gwiwar ofishin jakadancin Najeriya a Nijar da kuma Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM), domin tabbatar da dawowarsu cikin aminci da mutunci.

Waɗanda aka dawo da su sun haɗa da maza 174, mata 97, yara maza 137 da yara mata 89, kuma sun fito daga jihohi daban-daban ciki har da Kano, Jigawa, Borno da Kaduna.

Bayan isowarsu, an ba su abinci da tallafin gaggawa, sannan jami’an lafiya na Red Cross tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira sun duba masu matsalar lafiya.

NEMA ta ce bayan tantancewa da kammala rajista, za a tura su zuwa jihohinsu daban-daban.

Hukumar ta bayyana cewa yawancin waɗanda suka dawo sun bar Najeriya ne domin neman aikin yi da ingantacciyar rayuwa a ƙasashen waje, wasu ma suna shirin zuwa Libiya amma suka fuskanci matsaloli a hanya suka janye.

An shawarci ‘yan Najeriya da su guji bin hanyoyin ƙaura na haram saboda haɗarin rayuwa da suke tattare da su, musamman a hamada da ƙasashen da ba su da tsaro.

Wasu daga cikin waɗanda suka dawo sun bayyana irin wahalhalun da suka fuskanta, ciki har da ƙarancin abinci da ruwa, da kuma cin zarafi a tafiyar neman arziki.

Sun kuma roƙi gwamnati da ta taimaka musu da tallafin kuɗi ko jari domin su fara sabuwar rayuwa da kula da iyalansu.

0 $type={blogger}: