Hadarin Fashewar Gas a wajen hakar Ma’adinan Kwal na ƙasar China Ya Kashe Mutane 90.

Hadarin Fashewar Gas a wajen hakar Ma’adinan Kwal na ƙasar China Ya Kashe Mutane 90.

Akalla mutane 90 ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar gas a wani wurin hakan ma’adinan kwal da ke lardin Shanxi na arewacin kasar China.

Rahotanni sun bayyana cewa fashewar ta faru ne a ma’adinan Liushenyu da ke gundumar Qinyuan, yayin da ma’aikata 247 ke aiki a karkashin kasa a lokacin da abin ya faru. Hukumomi sun ce har yanzu ana ci gaba da aikin ceto domin gano wasu da suka bace.

Bayanai daga kafafen yada labarai na gwamnati sun ce hatsarin ya biyo bayan gano matakin iskar carbon monoxide da ya wuce kima a cikin ma’adinan kafin fashewar ta auku. 
Hukumomin China sun kama wani jami’in da ke kula da ma’adinan domin bincike kan musabbabin hadarin.

Shugaban kasar China ya yi kira ga dukkan hukumomi da su kara tsaurara matakan tsaron aiki a wurin hakan ma’adinai, tare da yin cikakken bincike domin hana sake afkuwar irin wannan mummunan lamari.

Lardin Shanxi shi ne babban yankin hakar kwal na China, kuma kasar na daga cikin manyan masu samarwa da amfani da kwal a duniya.

Wannan lamari ya zama mafi muni a bangaren hakan ma’adinai a China cikin sama da shekaru goma, lamarin da ya sake tayar da hankali kan matsalolin tsaro a masana’antar kwal ta kasar.

0 $type={blogger}: