Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba 27 ga Mayu da Alhamis 28 ga Mayu, 2026 a matsayin ranakun hutu domin bikin babban sallah (Eid-el-Kabir).
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin ta dauki matakin ne domin girmama muhimmancin addini da ruhin ibadar da Musulmai a Najeriya da sauran sassan duniya ke yi yayin bikin babban sallah (Eid-ul-Adha).
Ministan ya taya al’ummar Musulmi a Najeriya da mazauna kasashen waje murnar bikin, yana mai cewa Eid-ul-Adha na koyar da sadaukarwa da biyayya ga Allah da kuma tausayi ga bil’adama.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da lokacin hutun wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, tsaro, hadin kai da ci gaban kasa.
Tunji-Ojo ya kara da kira ga jama’a da su rungumi zaman lafiya da hadin kai da zaman tare cikin lumana yayin gudanar da bukukuwan Sallah, tare da yi wa Musulmai fatan bikin Eid-el-Kabir mai albarka da annashuwa.

0 $type={blogger}:
Post a Comment