Yakubu Gowon Ya Bayyana Dalilin Rubuta Tarihin Rayuwarsa Bayan Shekaru da Dama da barinsa kan mulki.

Yakubu Gowon Ya Bayyana Dalilin Rubuta Tarihin Rayuwarsa Bayan Shekaru da Dama da barinsa kan mulki.

Tsohon Shugaban Mulkin Sojan Najeriya, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya ce ya yanke shawarar wallafa tarihin rayuwarsa ne domin bai wa ‘yan Najeriya damar fahimtar dalilan da suka sa aka dauki wasu muhimman matakai a lokacin mulkinsa, musamman lokacin yakin basasar Najeriya.

Za a kaddamar da littafin tarihin ne a ranar 19 ga watan Mayu a Abuja, inda ake sa ran zai sake tayar da tattaunawa kan shugabanci, hadin kan kasa da kuma kalubalen mulki a daya daga cikin mafi wahalan lokuta a tarihin Najeriya.

Da yake magana kafin taron kaddamarwar, Gowon ya bayyana cewa manufarsa ba wai bude tsoffin raunuka ba ce, sai dai bayyana tunaninsa da dalilan da suka jagoranci wasu manufofi da matakai a lokacin da yake mulki.

Ya ce tarihin nasa yana nuna yadda ya yi kokarin gudanar da mulki cikin yanayi mai cike da kalubale da matsin lamba.

Littafin ya kunshi bayanai kan yarintarsa, rayuwarsa ta soja da yadda ya zama shugaban Najeriya a shekarar 1966 bayan rikicin siyasa da juyin mulki.

Babban bangare na littafin ya mayar da hankali kan yakin basasar Najeriya na tsakanin 1967 zuwa 1970, yakin da har yanzu yake da tasiri a siyasa da tarihin kasar.

Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron a matsayin babban bako na musamman, yayin da tsohon Ministan Tsaro Janar Theophilus Danjuma zai kaddamar da littafin mai shafuka 881.

Kamfanin Havilah Group da ya wallafa littafin ya bayyana aikin a matsayin muhimmiyar gudunmawa wajen adana tarihin Najeriya da bunkasa tattaunawar kasa.

Ana kuma sa ran manyan jami’an gwamnati da tsofaffin sojoji da jami’an diflomasiyya da shugabannin siyasa daga sassan kasar za su halarci bikin kaddamarwar a Abuja.

0 $type={blogger}: