Dangote Na Shirin Gina Babbar Matatar Mai a Kenya Domin Ƙarfafa Harkar Makamashi a Afirka

Dangote Na Shirin Gina Babbar Matatar Mai a Kenya Domin Ƙarfafa Harkar Makamashi a Afirka

Attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote, na shirin gina wata babbar matatar mai a Gabashin Afirka, inda birnin Mombasa na ƙasar Kenya ke kan gaba a matsayin wurin da ake son gudanar da aikin.

Rahotanni sun ce aikin zai ci tsakanin dala biliyan 15 zuwa 17, kuma zai yi kama da babbar matatar man Dangote da ke Lagos a Nigeria, wadda ta fara aiki gaba ɗaya a wannan shekara tare da samar da man fetur ga ƙasashe da dama a Afirka.

Shirin na zuwa ne yayin da ƙasashen Afirka ke neman hanyoyin ƙarfafa tsaron makamashi bayan rikice-rikicen duniya da suka shafi Iran da rufe mashigin Hormuz, wanda ke da muhimmanci wajen jigilar mai a duniya.

Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto, ya bayyana cewa ƙasashen Gabashin Afirka suna son rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje tare da amfani da albarkatun Afirka wajen bunƙasa masana’antu.

Ko da yake tun farko an tattauna gina matatar a tashar Tanga da ke Tanzania, Sai dai Dangote ya ce yanzu ya fi karkata ga Mombasa saboda tashar ruwanta mai zurfi da kuma girman tattalin arzikin Kenya.

Masana sun ce idan aka kammala aikin, zai taimaka wajen rage dogaro da shigo da man fetur daga Gabas ta Tsakiya, tare da samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki a yankin Gabashin Afirka.

Duk da yawan albarkatun mai da Afirka ke da su, har yanzu yawancin ƙasashen nahiyar na dogaro ne da shigo da tataccen mai saboda ƙarancin matatun mai. 
A yanzu haka Gabashin Afirka ba shi da wata matatar mai mai aiki duk da arzikin man da ƙasashe kamar Uganda da Sudan ta kudu ke da shi.

0 $type={blogger}: