Wata mata mai shekaru 28, Firdausi Musa, tare da ‘ya’yanta biyu da kuma mijinta, sun samu mummunan raunuka bayan da ake zargin kishiyarta ta watsa masu fetur tare da cinna musu wuta a jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a daren Litinin a yankin Hotoro da ke cikin birnin Kano, inda ake zargin wacce ake kira Maryam Muhammad ta zuba fetur a kan wadanda abin ya shafa kafin ta banka musu wuta.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya tayar da hankulan jama’a sosai, yayin da ake tsare da wacce ake zargi a ofishin ‘yan sanda na Mariri.
Firdausi Musa da ‘ya’yanta Khadija mai shekaru 7 da Ismail mai shekaru 3 na karɓar magani a asibitoci daban-daban a jihar Kano, ciki har da Asibitin Kwararru na Kashi na Dala da kuma Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad. Haka kuma mijin nasu, wanda ya yi yunkurin ceto su, shi ma ya samu raunuka.
Wani mutum ya ce rikicin cikin gida ne ya janyo lamarin, inda ya bayyana cewa Firdausi ta shigo gidan aure ne kwanan nan kuma ta rika kukan barazana daga kishiyar mijin.
Wata mata ta ce an sha tursasa wa wacce abin ya shafa kafin aukuwar lamarin, kuma ta bayyana cewa kishiyar ce ta aikata laifin yayin da take asibiti tana jinya.
Sai dai har yanzu Hukumomin ‘yan sandan Jihar Kano ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma ba zuwa lokacin hada wannan rahoto.

0 $type={blogger}:
Post a Comment