Shahararren Malamin Musulunci na jihar Kwara, Sheikh Abdulqadir Kamaludeen ya rasu

Shahararren Malamin Musulunci na jihar Kwara, Sheikh Abdulqadir Kamaludeen ya rasu

Shahararren malamin addinin Musulunci a Jihar Kwara, Sheikh Abdulqadir Muhammad Kamaludeen Al-Adabiy, wanda aka fi sani da Khalifatul-Adabiyah, ya rasu a garin Ilorin da safiyar Juma’a.

Rahotanni daga majiyoyi daban-daban, ciki har da sanarwar malamai a shafukan sada zumunta, sun tabbatar cewa marigayin ya rasu ne cikin daren Juma’a, abin da ya jawo alhini a fadin jihar da ma Najeriya baki ɗaya

Mutuwarsa ta tayar da hankulan al’ummar Musulmi da mazauna Ilorin baki ɗaya, inda malamai da shugabanni ke bayyana alhini da addu’o’in Allah ya jikansa.

Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga masarautar Ilorin da kuma ɗan’adam baki ɗaya. Ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa kuma ya saka shi Aljannatul Firdaus.

Sanata Saliu Mustapha, mai wakiltar Kwara ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, shi ma ya nuna alhini, inda ya ce rasuwar malamin babban rashi ce da ta shafi Musulmi da al’ummar Ilorin gaba ɗaya.

Marigayin shi ne babban ɗa da ya rage na Sheikh Muhammad Kamalud-deen, wanda ya kafa darikar Azumratul Adabiyyah Al-Kamoliyyah, wadda ta yi fice a fannin ilimin addinin Musulunci a Ilorin.

Ana sa ran za a fitar da sanarwar jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.

0 $type={blogger}: