Magajin Garin birnin London ya shiga sahun miliyoyin Musulmi wajen aikin Hajjin bana a ƙasar Saudi Arabia

Sadiq  Khan ya gudanar da aikin Hajjin bana a birnin Makkah na ƙasar Saudi Arabia, inda ya kasance tare da sama da Musulmai miliyan 1.5 daga sassan duniya.

Magajin Garin birnin London, Sadiq  Khan ya gudanar da aikin Hajjin bana a birnin Makkah na ƙasar Saudi Arabia, inda ya kasance tare da sama da Musulmai miliyan 1.5 daga sassan duniya.

Ya bayyana cewa wannan tafiya ta Hajji ta kasance mai matuƙar tasiri a rayuwarsa, yana mai cewa ta tunatar da shi muhimmancin daidaito da haɗin kai tsakanin mutane, ba tare da la’akari da ƙasa ko matsayi ko asali ba.

Aikin Hajji, wanda yake ɗaya daga cikin ginshiƙan Musulunci guda biyar, wajibi ne ga duk Musulmi da suka mallaki lafiya da kuma ikon kuɗi su gudanar da shi aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu. 
Aikin yana ƙunshe da jerin ibadu da ake gudanarwa a Makkah da kewaye cikin kwanaki da dama.

Kasancewar Sadiq Khan a cikin aikin hajjin bana ya sa ya shiga cikin miliyoyin mahajjata da ke taruwa a ɗaya daga cikin manyan tarurrukan addini mafi girma a duniya, wanda ke nuna girman wannan ibada da muhimmancinta a addinin Musulunci.

0 $type={blogger}: