Malamai da Daliban da aka yi garkuwan da su a jihar Oyo Sun bukaci gwamnati ta rayuwar su.

Malamai da Daliban da aka yi garkuwan da su a jihar Oyo Sun bukaci gwamnati ta rayuwar su.

Malamai da daliban makaranta da aka sace a Jihar Oyo sun bayyana a wani sabon bidiyo da masu garkuwa da su suka fitar, inda suka roki gwamnati ta biya bukatun masu garkuwar domin a sake su su koma gida lafiya.

A cikin bidiyon mai tsawon minti guda, an ga malamai mata biyu cikin tashin hankali sosai. 
Ɗaya ta yi magana da harshen Yoruba, yayin da wadda ke riƙe da jariri mai kimanin shekara biyu ta yi magana da Turanci. Duk wadanda aka yi garkuwa da su sun bayyana cikin tsoro da gajiya, bayan shafe kwanaki 13 a hannun masu garkuwa.

An ce wadanda lamarin ya shafa sun kasance cikin mutum 46 da aka sace a ranar 15 ga Mayu, 2026, lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a makarantar Community High School da ke Ahoro-Esinele da Yawota Baptist Nursery and Primary School a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo. 
Rahotanni sun nuna cewa an tafi da dalibai 39 tare da malamai bakwai.

A cikin bidiyon, wata malama ta yi kira cikin harshen Yoruba tana rokon gwamnati da ta nuna tausayi tare da gujewa amfani da karfi, tana mai cewa suna cikin wahala mai tsanani a cikin daji, inda aka bar su cikin ruwan sama da rana, tare da yara da manya.

Wata malama kuma ta yi magana cikin Turanci kai tsaye ga Gwamna Seyi Makinde, tana rokon gwamnati da ta shiga tattaunawa da masu garkuwar da su, tare da yin duk abin da ya dace domin ceton rayukansu.

Bayan faruwar lamarin, kungiyoyin malamai da kungiyoyin kare hakkin jama’a a jihar Oyo sun gudanar da zanga-zangar lumana, suna neman gwamnati ta dauki matakin gaggawa domin ceto wadanda aka sace. 
Kungiyar malamai ta Najeriya ta ce dole ne a kara tsaro a makarantun gwamnati.

Kungiyar ta bayyana damuwa sosai musamman ganin cewa akwai ƙanana yara sosai a cikin wadanda aka sace, tana mai cewa bai kamata yara su kasance cikin irin wannan hatsari ba.

A nata bangaren, gwamnatin jihar Oyo ta bayyana cewa ana ci gaba da kokarin ceto wadanda abin ya shafa. Mai ba gwamna shawara kan harkokin tsaro ya tabbatar wa masu zanga-zanga cewa gwamnati tana aiki tukuru kan lamarin, amma ya ce ba za a iya bayyana duk bayanai ba saboda dalilan tsaro da kuma gudun kawo cikas ga aikin ceto.

0 $type={blogger}: