Majalisar Dokokin Ghana ta sake amincewa da wata doka mai cike da ce-ce-ku-ce wadda ke ƙara tsaurara matakai kan aure jinsi daya, LGBTQ, inda yanzu ake jiran sa hannun Shugaban Ƙasar John Mahama domin ta zama doka.
Sabuwar dokar, wadda ake kira Dokar Kare Darajojin Iyali da Haƙƙin Jima’i, ta tanadi hukuncin daurin shekaru uku ga duk wanda aka samu yana shiga hulɗar jinsi daya. Haka kuma, tana tanadar da hukuncin ɗaurin shekaru uku zuwa biyar ga duk wanda aka samu yana tallatawa ko ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan jinsi daa (LGBTQ).
Tun a shekarar 2024 ne Majalisar Dokokin ƙasar ta fara amincewa da irin wannan doka baki ɗaya, amma tsohon shugaban ƙasa, Nana Akufo-Addo, bai sanya hannu a kanta ba kafin wa’adinsa ya ƙare.
Bisa kundin tsarin mulkin Ghana, duk wata doka da shugaban ƙasa bai sanya wa hannu ba kafin ƙarshen wa’adin majalisa, za ta zama ba ta da inganci har sai sabuwar majalisa ta sake nazari a kanta.
Sabuwar dokar da aka amince da ita ta ci gaba da ɗauke da mafi yawan tanade-tanaden da ke cikin tsohuwar dokar, sai dai ta ƙara wasu keɓancewa ga ma’aikatan lafiya da lauyoyi da kuma ‘yan jarida yayin gudanar da aikinsu.
A halin yanzu, dokokin Ghana sun haramta hulɗar jinsi daya tun daga zamanin mulkin mallaka na Birtaniya. Duk da haka, ba a samu rahoton gurfanar da wani a kotu bisa wannan doka ba zuwa yanzu.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa sun yi Allah-wadai da wannan doka, suna mai cewa za ta iya ƙara nuna wariya da tauye haƙƙin mutanen da ke cikin al’ummar ta LGBTQ.
Idan shugaban ƙasa ya sanya hannu a kanta, dokar za ta kasance cikin mafi tsauraran dokokin hana harkokin jinsi Daya, LGBTQ a nahiyar Afirka.

0 $type={blogger}:
Post a Comment