Pantami Ya Fice Daga APC, Ya Samu Tikitin Gwamnan PDP A Gombe

Pantami Ya Fice Daga APC, Ya Samu Tikitin Gwamnan PDP A Gombe

Tsohon ministan sadarwa da ci gaban fasahar zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP, inda ya samu tikitin takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar.

Pantami ya zama ɗan takara ne bayan zaɓen fidda gwani da PDP ta gudanar a yau Talata a Gombe, inda aka tabbatar da shi ta hanyar amincewar baki ɗaya saboda kasancewarsa shi kaɗai a takarar.

Shugaban kwamitin zaɓen PDP, Gregory Yenlong, ne ya bayyana Pantami a matsayin wanda zai wakilci jam’iyyar a zaɓen gwamna na shekarar 2027.

Da yake jawabi bayan bayyana sakamakon, Pantami ya ce ya shiga takarar ne domin yi wa al’ummar jihar Gombe hidima. Ya kuma yi alƙawarin gudanar da mulki cikin adalci da gaskiya idan aka zaɓe shi a matsayin gwamna.

Yanzu haka Pantami zai fafata da Jamilu Gwamna, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar.

Kafin ficewarsa daga APC, Pantami ya soki yadda aka zaɓi Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar sulhu na jam’iyyar. Duk da cewa ya nemi a gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye, daga baya ya janye daga takarar yana zargin rashin gaskiya da sahihanci a tsarin zaɓen.

Sauya shekar Pantami zuwa PDP ya haifar da ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar, inda wasu masu neman takarar gwamna suka nuna adawa da shigarsa cikin takarar.

A cikin wata sanarwa bayan wani taron gaggawa a Gombe, wasu ‘yan takarar PDP guda huɗu — Abdulkadir Hamma Saleh da Khamisu Ahmed Mailantarki da Usman Aliyu Garry da Monica Kaltho — sun ce dokar zaɓe ba ta yarda wanda ya shiga zaɓen fidda gwani a wata jam’iyya ya sake shiga wata jam’iyyar domin ci gaba da takara ba.

Sai dai duk da wannan adawa, shugabannin PDP a jihar sun amince da Pantami a matsayin wanda ya dace ya jagoranci jam’iyyar a zaɓen gwamna mai zuwa.

0 $type={blogger}: