Hare-haren Isra’ila Kan Sansanin ‘Yan Gudun Hijira a Gaza Sun Kashe Falasdinawa Bakwai.

Hare-haren Isra’ila Kan Sansanin ‘Yan Gudun Hijira a Gaza Sun Kashe Falasdinawa Bakwai.

Akalla Falasdinawa bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon sabbin hare-haren sama da Isra’ila ta kai a sassa daban-daban na Gaza, a cewar jami’an lafiya na Falasdinawa, duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma.

Rahotanni sun bayyana cewa mutum biyar daga cikin waɗanda suka mutu sun rasa rayukansu ne bayan wani hari da jirgin sama maras matuki na Isra’ila ya kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Maghazi da ke tsakiyar Gaza a yau Talata.

Jami’an kare fararen hula sun ce wasu mutane da dama sun jikkata a harin, inda aka garzaya da su asibitoci domin samun kulawa.

Hukumomin Asibitin Al-Aqsa sun tabbatar da adadin waɗanda suka mutu a harin.

Rahotannin cikin gida sun nuna cewa harin na iya kasancewa an kai shi ne kan wasu Falasdinawa da suka yi arangama da wata ƙungiya mai ɗauke da makamai da ake zargin Isra’ila na mara wa baya a gabashin sansanin.

A kudancin Gaza kuwa, wasu mutum biyu sun mutu bayan wani hari da Isra’ila ta kai kan wata mota a birnin Khan Younis. Likitoci sun ce wasu da dama sun samu raunuka a harin.

Sabbin hare-haren na zuwa ne a lokacin da ake shirye-shiryen bukukuwan Babbar Sallah da kuma ci gaba da zaman ɗar-ɗar kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka da Qatar suka shiga tsakani wajen samarwa.

A cewar jami’an Falasdinawa, sama da mutum 900 aka kashe tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wutar a watan Oktoban 2025.

Isra’ila ma ta ce sojojinta huɗu sun mutu yayin fafatawa da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na Falasdinawa tun bayan yarjejeniyar.

A baya Isra’ila ta taɓa amincewa cewa tana goyon bayan wasu ƙungiyoyi masu adawa da Hamas a wasu yankunan Gaza, lamarin da masu suka ke cewa yana ƙara haddasa rikici da rarrabuwar kawuna a yankin.

0 $type={blogger}: