Masu amfani da addini wajen kisa za su fuskanci azabar Allah – Sarkin Musulmi

Masu amfani da addini wajen kisa za su fuskanci azabar Allah – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya yi kakkausar suka ga mutanen da ke kashe rayukan mutane marasa laifi suna amfani da sunayen addini, inda ya ce irin waɗannan mutane za su fuskanci hukuncin Allah a lahira.

Yayin da yake magana a taron Majalisar Addinai ta Kasa (NIREC) da aka gudanar a Abuja, Sarkin Musulmi ya jaddada cewa bai kamata a danganta laifuka da addini ba, domin duk wanda ya aikata laifi shi ne mai laifi, ba addininsa ba.

Ya ce, rikice-rikicen da ake dangantawa da addini a Najeriya galibi ba su da tushe na addini, kuma wannan kuskuren na ƙara rura wutar rashin fahimta tsakanin al’umma.

A cewarsa, duk wanda ya kashe mutane marasa laifi yana kiran sunan Allah yana yin abin da ya saba wa koyarwar addini, kuma hakan babban zunubi ne.

“Ba za ka kashe rayukan mutane ba sannan ka ce kana bauta wa Allah. Duk wanda ya yi hakan ba ya bin hanyar Allah,” in ji shi.

Sarkin Musulmi ya kuma gargadi mutane kan yin amfani da addini ta hanyar da ba daidai ba, yana mai cewa sanin Larabci ko furucin addini ba ya nufin mutum malami ne ko shugaba na addini.

Taron ya samu halartar manyan shugabannin addini da gwamnati, ciki har da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Christian Association of Nigeria, da kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji tsattsauran ra’ayi, su rungumi zaman lafiya, fahimtar juna da kuma hadin kai tsakanin mabiya addinai daban-daban.

0 $type={blogger}: