Wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, na da cikakken damar tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Wannan hukunci ya biyo bayan ƙarar da wani Johnmary Jideobi ya shigar, yana neman kotu ta hana Jonathan tsayawa takara ko kuma kowace jam’iyya ta gabatar da shi a matsayin ɗan takara. Haka kuma, mai ƙarar ya buƙaci a hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) karɓa ko wallafa sunan Jonathan a matsayin ɗan takara.
Alƙali Peter Lifu, wanda ya yanke hukuncin, ya yi watsi da ƙarar gaba ɗaya, yana mai cewa Jonathan na da hurumin tsayawa takara a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Najeriya. Kotun ta kuma bayyana cewa akwai wasu hukunce-hukunce na baya da suka riga suka tabbatar da cancantar sa.
Alƙalin ya bayyana ƙarar a matsayin wadda aka shigar ba bisa ƙa’ida ba, kuma ya ce mai ƙarar ba shi da hurumin shari’a domin bai nuna wata cutuwa ta kai tsaye da lamarin ya jawo masa ba.
Bugu da ƙari, kotun ta ci tarar mai ƙarar saboda shigar ƙarar da ta bayyana a matsayin marar tushe, tare da ƙin amincewa da buƙatar da ya yi na a janye alkali daga shari’ar.
Wannan hukunci ya warware shakku kan makomar siyasar Jonathan, tare da tabbatar da cewa yana da damar shiga takarar zaɓen 2027.

0 $type={blogger}:
Post a Comment