Gwamnatin Jihar Kano ta amince da bayar da tallafin Naira 20,000 ga ma’aikatan gwamnati a fadin jihar da kananan hukumomi 44 domin taya su murnar bukukuwan Eid-el-Kabir.
Wannan sanarwa ta fito ne cikin wata takarda da aka fitar a Kano daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, ta hannun Kakakin Yada Labarai, Musa Tanko-Muhammad.
A cewar sanarwar, an kirkiro wannan tallafi ne domin taimaka wa ma’aikata wajen rage matsin tattalin arziki yayin bukukuwan Sallah.
Za a bai wa ma’aikatan da ke matakin albashi na Grade Level 01 zuwa 14 a ma’aikatu da hukumomi da kananan hukumomi a fadin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnatinsa na inganta jin dadin ma’aikata, wadanda ya kira ginshikin aikin gwamnati.
Ya kara da cewa an dauki wannan mataki ne saboda halin da ake ciki na matsin tattalin arziki da kuma yawan bukatun da ke tasowa a lokutan bukukuwa.
Gwamnan ya ce tallafin zai taimaka wa ma’aikata wajen yin bukukuwan sallar idi cikin walwala tare da iyalansu.
Haka kuma ya taya ma’aikata da sauran al’ummar jihar Kano murnar Sallah, yana mai addu’ar zaman lafiya da hadin kai da cigaba a jihar da kasa baki daya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment