Fiye da mahajjata Musulmi miliyan 1.6 ne suka taru a yau Talata a Filin Arafat da ke ƙasar Saudiyya domin gudanar da mafi muhimmanci kuma mafi tsarkakakken bangare na aikin Hajjin bana.
Ranar Arafah ana ɗaukarta a matsayin mafi girman rana a aikin Hajji, inda mahajjata ke shafe yini suna ibada da karatun Alƙur’ani da addu’o’i da neman gafarar Allah.
Tun daga wayewar gari, mahajjata suka rika isa filin na Arafat, wanda ke kusan kilomita 20 daga birnin Makkah, inda zasu ci gaba da gudanar da ibada har zuwa faduwar rana.
Tsayuwar Arafat, wacce ake kira Wuƙufin Arafah, ita ce ginshiƙin aikin Hajji. A cikin hadisai, Annabi Muhammad (SAW) ya bayyana muhimmancin wannan rana da cewa: “Hajji shi ne Arafah.”
Da tsakar rana, za'a gabatar da hudubar Arafah ga mahajjata, sannan su haɗa sallolin Azahar da La’asar tare da takaitawa kamar yadda Sunnah ta tanada. Mahajjatan sun ci gaba da yin addu’o’i da tasbihi da neman gafara cikin yanayi na tawali’u da nutsuwar zuciya.
Filin Arafat, musamman Jabalur Rahmah (Dutsen Rahama), na da muhimmanci sosai a addinin Musulunci, domin ana danganta shi da rahama da gafarar Allah, tare da kasancewa wurin da Annabi Muhammad (SAW) ya gabatar da hudubarsa ta bankwana.
Mahukuntan Saudiyya sun girke jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya da motocin agaji domin kula da lafiyar mahajjata da sauƙaƙa zirga-zirgarsu, musamman yayin da yanayin zafi ya haura digiri 45 na Celsius.
Bayan faduwar rana, mahajjata zasu fara barin filin na Arafat zuwa Muzdalifah domin gudanar da sallolin Magariba da Isha’i tare, kafin su kwana a can domin ci gaba da sauran ayyukan aikin Hajji a Mina.

0 $type={blogger}:
Post a Comment