Jiragen Ruwan Yakin Amurka Za Su Fuskanci mummunar Martani Idan Aka Sake Kai wa Iran Hari - kwamandan IRGC.

Jiragen Ruwan Yakin Amurka Za Su Fuskanci mummunar Martani Idan Aka Sake Kai wa Iran Hari - kwamandan IRGC.

Wani babban kwamandan rundunar juyin juya halin Musuluncin ƙasar Iran ta IRGC, ya yi gargadin cewa duk wani sabon harin soja da Amurka za ta kai kan Iran zai jawo mummunar martani mai ɗaukar lokaci, ciki har da kai hare-hare kan jiragen ruwan yakin Amurka.

Brigadier Janar Seyyed Majid Mousavi, kwamandan rundunar sararin samaniyar IRGC, ya fitar da wannan gargadi ne bayan rahotannin cewa Rundunar sojin Amurka dake yankin gabas ta tsakiya (CENTCOM) na nazarin shirye-shiryen kai hare-hare gajeru kan cibiyoyin more rayuwa na Iran.

“Kun ga abin da ya faru da sansanoninku a yankin; jiragen ruwanku ma za su fuskanci irin wannan kaddara,” in ji Mousavi.

Rahotanni sun nuna cewa shugaban Amurka Donald Trump yana duba sabbin tsare-tsaren soja da kwamandan CENTCOM Admiral Brad Cooper ya gabatar masa. Wadannan tsare-tsaren sun hada da kai hare-hare kan Iran da kuma wasu zabuka masu tsauri kamar kwace iko da wani bangare na mashigar ruwan Hormuz domin bude hanyoyin kasuwanci na ruwa.

Har ila yau, ana zargin akwai wani shiri na tura sojoji na musamman domin kwace ajiyar uranium mai wadatar gaske na Iran.

Trump ya kuma bayyana cewa toshe hanyoyin ruwa (naval blockade) na iya zama mafi tasiri fiye da kai hari kai tsaye, amma har yanzu yana la’akari da amfani da karfin soja idan tattaunawa ta kasa cimma nasara.

Jami’an Iran sun ce kasar ta riga ta nuna karfinta ta hanyar kai hare-haren ramuwar gayya kan sojojin Amurka da na Isra’ila bayan hare-haren da aka kai mata a baya. Sun kuma jaddada cewa duk wani sabon hari zai fuskanci “martani mai radadi da kuma nisa.”

Sauran jami’an IRGC sun yi gargadi cewa Iran na da sabbin fasahohin yaki da ba a bayyana ba, ciki har da tsarin harbi na (smart targeting), wanda za a iya amfani da shi kan sojojin Amurka idan rikici ya sake barkewa.

Kwamandan rundunar ruwan Iran, Rear Admiral Shahram Irani, ya kuma nuna cewa nan ba da jimawa ba kasar za ta bayyana wani sabon makami da abokan gaba za su ji tsoronsa.

Har yanzu ana cikin tsaka mai wuya bayan rushewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, tare da ci gaba da takaddama kan tsaron hanyoyin ruwa, musamman a muhimmin mashigin ruwan ta Hormuz.

0 $type={blogger}: