Gwamnatin Kano za ta yi gwajin lafiya ga ma’aurata 3,000 kafin auren bai daya.

Gwamnatin Kano za ta yi gwajin lafiya ga ma’aurata 3,000 kafin auren bai daya.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da cewa za ta fara gudanar da gwajin lafiya ga ma’aurata 3,000 da ake shirin daura musu aure a karkashin shirin auren bai daya na gwamnati.

Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Mujahedeen Aminudeen, ya bayyana haka ne a tattaunawar sa da manema labarai, inda ya ce shirin zai kunshi maza 1,500 da mata 1,500 da aka zaba.

Ya ce manufar gwajin ita ce tantance lafiyar ma’auratan kafin a daura aurensu. Gwajin zai hada da cutar kanjamau (HIV/AIDS), hepatitis da gwajin kwayoyin halitta (genotype), da kuma gwajin amfani da kwayoyi.

Aminudeen ya kara da cewa gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ce ke shirya wannan auren bai daya domin tallafa wa marasa galihu, ciki har da zawarawa da matan da aka sake su, da kuma ‘yan mata marasa aure.

Ya bayyana cewa gwamnati za ta taimaka wa amaryu da kayan daki kamar gadaje da katifa da filo, tare da ba su kudin jari domin fara kananan sana’o’i bayan aure, baya ga kudin sadaki da gwamnati za ta biya.

Ya gargadi cewa halartar gwajin lafiya wajibi ne ga duk wanda ke son shiga shirin, kuma duk wanda bai yi ba za a cire shi daga cikin wadanda za su amfana.

An fara shirin auren bai daya ne tun zamanin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin wani mataki na tallafa wa al’umma da rage matsalolin zamantakewa a jihar.

0 $type={blogger}: