Fursunoni 9 a Kano Sun Kammala Haddar Alƙur’ani Mai Girma

Fursunoni 9 a Kano Sun Kammala Haddar Alƙur’ani Mai Girma

Fursunoni tara da ke zaman hukunci a cibiyar gyaran hali da ke Wudil a Kano sun samu nasarar kammala haddar Alƙur’ani Mai Girma.

Wannan gagarumin nasara ta zo ne daidai da bikin cika shekaru 50 da kafuwar cibiyar.

Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS) reshen Jihar Kano, Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya bayyana cewa wasu daga cikin fursunonin ba su da cikakkiyar ilimin karatun Alƙur’ani lokacin da aka kawo su cibiyar. 
Sai dai ta hanyar jajircewa da ladabi da kuma tsari mai kyau na koyarwa, suka samu damar kammala haddar.

Ya ce wannan nasara na nuna irin ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen gyaran hali da tarbiyya da kuma dawo da fursunoni cikin al’umma, daidai da dokar Hukumar Gyaran Hali ta shekarar 2019.

Haka kuma, ya ce cibiyar Wudil ta dade tana zama abin koyi, inda ake bai wa fursunoni ilimi da koyon sana’o’i da shirye-shiryen tarbiyya domin canza rayuwarsu.

Kwanturolan Hukumar Gyaran Hali na Jihar Kano, Ahmed Yusuf Lakpene, ya yaba wa Shugaban Hukumar na ƙasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa manufofin da yake aiwatarwa na inganta ilimi da koyon sana’o’i a cibiyoyin tsare fursunoni a faɗin ƙasar nan.

Shi ma jami’in da ke kula da cibiyar, Ibrahim Wada Ibrahim, ya bayyana wannan nasara a matsayin sakamakon kyakkyawan shugabanci da kuma jajircewa wajen bunƙasa rayuwar fursunoni.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Jami’ar Aliko Dangote ta Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Farfesa Musa Tukur Yakasai, ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa yana taka muhimmiyar rawa wajen mayar da fursunoni masu amfani ga al’umma.

0 $type={blogger}: