Kotu a Uganda ta yanke hukuncin kisa kan mutumin da ya kashe yara huɗu a makarantar yara.

Kotu a Uganda ta yanke hukuncin kisa kan mutumin da ya kashe yara huɗu a makarantar yara.

Wata kotu a Kampala, Uganda, ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa bayan an same shi da laifin kashe ƙananan yara huɗu a wani mummunan hari da ya faru a makarantar yara (nursery) a farkon watan Afrilu.

Mutumin, Christopher Okello Onyum, an zarge shi da kashe yaran masu shekaru tsakanin shekara ɗaya zuwa uku ta hanyar daba musu wuka. Rahotanni sun nuna cewa ya shiga makarantar ne ta hanyar yin kamar shi ɗaya ne daga cikin iyaye, sannan ya kulle ƙofar makarantar kafin ya aiwatar da harin cikin ɗan lokaci kaɗan.

Jami’an tsaro sun ce wasu iyaye da suka fusata sun yi yunƙurin kai masa hari, amma wani jami’in tsaro ya dakatar da su, sannan aka kama shi.

A yayin shari’ar, an gabatar da hujjoji da ke nuna cewa Onyum ya binciki “makarantu da ke kusa da shi” da kuma wasu abubuwan tashin hankali a intanet kafin harin, wanda ke nuna cewa ya shirya aikata laifin tun da farko. 
Kotu ta yi watsi da hujjar da ya bayar cewa yana cikin rashin hankali a lokacin da ya aikata laifin, inda alkalin ya bayyana cewa yadda aka aiwatar da kisan ya nuna tsantsar shiri da niyya.

Har ila yau, alkalin ya lura cewa mutumin bai nuna nadama ba kuma bai nemi gafarar iyayen yaran da aka kashe ba.

Wata ma’aikaciyar makarantar da ta ba da shaida ta bayyana irin halin da ta tsinci kanta ciki, inda ta ce ta ga ɗaya daga cikin yaran cikin jini, sannan ta yi ƙoƙarin taimakawa amma mutumin ya yi yunƙurin kai mata hari kafin ta samu damar tserewa.

Duk da cewa dokar Uganda na amincewa da hukuncin kisa, ba a cika aiwatar da shi ba, domin an daina aiwatar da irin wannan hukunci sama da shekaru 20 da suka gabata.

0 $type={blogger}: