Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, a matsayin shugaban jam’iyyar ADC, bayan rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar.
A hukuncin da alkalai biyar suka yanke baki ɗaya a yau Alhamis, karkashin jagorancin Mai shari’a Mohammed Lawal Garba, kotun ta soke umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja wanda ya buƙaci a koma yadda al’amura suke a baya.
Kotun Koli ta bayyana cewa umarnin kotun ɗaukaka ƙarar bai zama dole ba, kuma bai bi ka’ida ba.
Ta kuma ƙara da cewa ƙarar da aka shigar kan batun hurumin kotu ba ta cika sharuddan doka ba, domin an shigar da ita ne daga wani umarni na gaggawa ba tare da samun izinin kotu ba.
Hukuncin ya kuma soke cire shugabancin Mark da aka yi daga rajistar jam’iyya a jadawalin INEC, tare da tabbatar da dawowarsa kan muƙaminsa.

0 $type={blogger}:
Post a Comment