Gwamnatin Jihar Kwara ta kaddamar da jigilar mahajjata na shekarar 2026, inda ta tura rukuni na farko na mutane 374 zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.
Mahajjatan sun tashi ne daga filin jirgin sama na General Tunde Idi-Agbon da ke Ilorin a yau Laraba da misalin karfe 3 na rana, cikin jirgin Max Air, inda suka nufi birnin Madina kai tsaye.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Rafiu Ajakaye, ya fitar, jimillar mahajjata 1,714 daga jihar Kwara ne za su gudanar da Hajjin bana.
Yayin da ake yi wa mahajjatan bankwana, wakilin gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, Saadu Salaudeen, ya bukaci su kasance masu ladabi da kyawawan halaye, tare da wakiltar jihar Kwara da Najeriya da mutunci a kasar Saudiyya.
Ya kuma jaddada muhimmancin bin dokoki da ka’idojin kasar da suke ziyarta.
Haka zalika, ya bukace su da su yi addu’o’i domin zaman lafiya da hadin kai a Najeriya, musamman a jihar Kwara, tare da bin umarnin shugabannin tawagar Hajji da sauran jami’ai.
A nasa bangaren, Amirul Hajj kuma Etsu Tsaragi, Abdullahi Aliyu, ya tabbatar da cewa za su kula da jin dadin mahajjatan tare da tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.
Shi ma Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara, Abdulkadir Abdulsalam, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa goyon bayan da ta bayar. Ya ce an hada da likitoci da nas-nas cikin tawagar domin kula da lafiyar mahajjatan.
Ya kara da cewa an kuma tanadi abinci na gargajiya domin mahajjatan su samu sauki da jin dadin zama yayin da suke kasar Saudiyya.
Ana sa ran za a ci gaba da jigilar sauran mahajjata daga jihar a cikin kwanaki masu zuwa.
.jpeg)
0 $type={blogger}:
Post a Comment