Wanda Ya Kafa tashar watsa labarai ta CNN, Ted Turner, Ya Rasu Yana Da Shekaru 87.

Wanda Ya Kafa tashar watsa labarai ta CNN, Ted Turner, Ya Rasu Yana Da Shekaru 87.

Ted Turner, fitaccen ɗan kasuwar Amurka kuma gwarzon kafafen yaɗa labarai wanda ya sauya tsarin watsa labarai a duniya ta hanyar ƙirƙirar tashar CNN a shekarar 1980, ya rasu yana da shekaru 87.

An ruwaito cewa ya dade yana fama da cutar Lewy Body Dementia, wadda ke lalata ƙwaƙwalwa a hankali.

Kafuwar CNN ta kawo sauyi mai girma a aikin jarida, inda ta fara watsa labarai ba tare da tsayawa ba na awa 24, abin da ya sauya yadda ake isar da labarai a duniya. Tashar ta yi fice sosai yayin yaƙin Gulf, inda ta rika kawo rahotanni kai tsaye daga wuraren yaƙi.

CNN ta zama muhimmiyar majiya ta labarai, tana rufe manyan abubuwan duniya kamar rushewar Tarayyar Soviet da kuma tarzomar Tiananmen Square a birnin Bejin na ƙasar Sin.

An haifi Turner a Cincinnati, Ohio, a shekarar 1938. Ya karɓi ragamar kasuwancin iyalinsa kafin ya faɗaɗa shi zuwa harkar watsa labarai. Sayen wata ƙaramar tashar talabijin a Atlanta a 1970 ne ya zama tushen gina babbar daular sa.

Baya ga CNN, ya mallaki wasu manyan tashoshi na nishaɗi da wasanni, kuma nasarorin sa sun zaburar da kafuwar wasu tashoshin labarai irin su Fox News wanda Rupert Murdoch ya kafa.

An yi ta miƙa ta’aziyya daga sassa daban-daban, inda shugabannin CNN suka bayyana shi a matsayin mutum mai hangen nesa wanda gudunmawarsa za ta ci gaba da tasiri a fannin jarida da kafafen yaɗa labarai a duniya.

0 $type={blogger}: