Sojojin Najeriya sun ceto mutane 9 da aka yi garkuwa da su a jihar Kogi, tare da kama wani mai safarar makamai.

Sojojin Najeriya sun ceto mutane 9 da aka yi garkuwa da su a jihar Kogi, tare da kama wani mai safarar makamai.

Rundunar Sojojin Najeriya ta Birgediya ta 12 ta samu nasarar ceto mutane tara da aka yi garkuwa da su tare da dakile wata harkar safarar makamai da ake zargin tana da alaƙa da ‘yan ta’adda a jihar Kogi.

Ayyukan ceto da aka gudanar a ranar 6 ga Mayu, 2026 sun haifar da cafke wani mutum da ake zargi yana safarar alburusai a ɓoye cikin kayan masara.

Kakakin rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi, ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne bisa sahihin bayanan sirri da kuma ci gaba da matsin lamba kan masu laifi a yankin.

Mutanen da aka ceto sun haɗa da yara maza biyar, ‘yan mata biyu da kuma mata manya biyu da ake zargin suna da alaƙa da harin da aka kai ma wani gidan marayu a jihar kwanan nan. An same su a yankin daji na Agbaja da ke ƙaramar hukumar Lokoja.

An garzaya da su asibitin soja inda aka ba su kulawa ta gaggawa, kuma rahotanni sun tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya.

A wani samame daban da aka gudanar a kan hanyar Obajana zuwa Lokoja, sojoji sun kama wani mutum mai suna Yahaya Umar da ake zargi da safarar harsasai 500 na 7.62mm NATO da aka ɓoye cikin buhun masara.

Bincike na farko ya nuna cewa yana cikin wata ƙungiyar da ke safarar makamai ga ‘yan ta’adda a yankin Arewa ta Tsakiya. An ce harsasan suna kan hanyar zuwa jihar Neja ne domin isar da su ga wani wanda ba a bayyana sunansa ba.

Hukumomin soji sun ce ana ci gaba da bincike kan wanda ake zargin, yayin da ake ƙoƙarin gano sauran membobin ƙungiyar.

Rundunar ta bayyana waɗannan nasarori a matsayin wani ɓangare na aikin “Operation Tiger Paw II” da ke da nufin kawar da hanyoyin samar da makamai ga ‘yan ta’adda da kuma inganta tsaro a yankin.

Sojojin sun kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimaka wa hukumomi wajen yaki da laifuka.

0 $type={blogger}: