Hisbah Ta Kama Wani Namiji Da Aka Boye Cikin Jakar “Ghana Must-Go” A Gidan Matar Aure A Kebbi

Hisbah Ta Kama Wani Namiji Da Aka Boye Cikin Jakar “Ghana Must-Go” A Gidan Matar Aure A Kebbi

Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi ta kama wani mutum da ake zargin an same shi a boye cikin jakar “Ghana Must-Go” a gidan wata matar aure da ke unguwar Badariya a Birnin Kebbi.

Daraktan Shari’a na hukumar, Sirajo Kamba, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 19 ga Mayu, 2026.

A cewarsa, mazauna yankin ne suka sanar da jami’an Hisbah da misalin karfe 12:15 na dare bayan sun ga wani namiji ya shiga gidan matar, lamarin da ya sa suka fara zargin aikata abin da ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.

Kamba ya bayyana cewa nan take jami’an Hisbah suka garzaya gidan domin gudanar da bincike.

Ya ce da jami’an suka isa gidan, sun nemi izinin yin bincike amma matar ta fara musanta cewa akwai wani mutum a cikin gidan.

Sai dai daga bisani ta amince a bincika gidan, inda jami’an suka gano mutumin a boye cikin wata babbar jakar tafiya da aka fi sani da “Ghana Must-Go”.

Daraktan ya kara da cewa binciken farko ya nuna akwai alakar soyayya tsakanin mutumin da matar auren.

A cewarsa, mutanen biyu sun amsa zargin da ake musu yayin tambayoyi, kuma ana sa ran za a gurfanar da su a kotun Shari’a domin fuskantar hukunci bisa dokokin Musulunci.

0 $type={blogger}: