Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu bayan wasu matasa biyu dauke da makamai suka bude wuta a wani masallaci da ke San Diego, a wani hari da hukumomi ke zargin nuna kiyayya ga Musulmi.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar Litinin a cibiyar Musulunci ta "Islamic Center of San Diego", inda maharan suka shiga harabar masallacin suka fara harbe-harbe, lamarin da ya jawo daukin jami’an tsaro masu yawa.
Babban jami’in ‘yan sandan San Diego, Scott Wahl, ya ce jami’ansu sun isa wurin cikin mintuna kadan bayan samun rahoton harin.
Ya bayyana cewa tun da farko mahaifiyar daya daga cikin wadanda ake zargi ta sanar da ‘yan sanda cewa danta ya bace kuma yana cikin yanayin damuwa, tare da bayanin cewa wasu bindigogi da mota sun bace daga gidanta.
Da jami’an tsaro suka isa masallacin, sun tarar da gawar mutane uku a wajen ginin, ciki har da wani jami’in tsaro mai suna Amin Abdullah, wanda hukumomi suka yabawa bisa kokarin da ya yi wajen kare mutane yayin harin.
Wahl ya ce matashin jami’in tsaron ya taka muhimmiyar rawa wajen hana harin yin muni fiye da haka.
Daga bisani an gano maharan biyu, masu shekaru 17 da 19, a mace cikin wata mota da ke kusa da wurin, bayan da ake zargin sun kashe kansu.
Hukumomi sun ce sun gano wata takarda dauke da kalaman kiyayya, abin da ya kara karfafa zargin cewa harin na da nasaba da kyamar Musulmi.
Masallacin na Islamic Center of San Diego na daga cikin manyan cibiyoyin Musulunci a yankin, kuma yana daukar dubban masu ibada tare da makarantar yara.
Kungiyoyi masu kare hakkin Musulmi ciki har da Council on American-Islamic Relations sun yi Allah wadai da harin tare da kira ga hukumomi su gudanar da cikakken bincike.
Haka kuma gwamnan jihar California, Gavin Newsom, ya ce babu gurbin kiyayya ko tashin hankali a jihar.
Harin ya faru ne kwanaki kadan kafin bukukuwan Eid al-Adha da kuma aikin Hajji na 2026.

0 $type={blogger}:
Post a Comment