Wani harin sama da Isra’ila ta kai a daren Litini a kudancin Lebanon, ya hallaka aƙalla mutane shida, tare da jikkata wasu mutum bakwai, Kamar yadda kafafen yaɗa labarai na Lebanon suka ruwaito.
Harin ya zo ne a cikin jerin hare-hare da Israi'la ke kaiwa kusan kowace rana duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka ta shiga tsakani, wadda har yanzu ba ta dakatar da rikicin yadda ya kamata ba.
Hukumomin Lebanon sun ce ɗaruruwan mutane ne suka mutu tun lokacin da aka fara wannan yarjejeniyar, yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a kudanci da gabashin ƙasar.
Bayan harin, sojojin Isra’ila sun fitar da sabbin umarnin barin gidaje ga wasu garuruwa a kudancin Lebanon da yankin Bekaa, abin da ke nuna yiwuwar ƙarin hare-haren. Rahotanni kuma sun ce an lalata muhimman abubuwan more rayuwa, ciki har da tashar famfo ruwa kusa da kogin Litani, da kuma gidaje a yankunan iyaka.
Mazauna yankunan da abin ya shafa sun rabu tsakanin guduwa da kuma ci gaba da zama, duk da ƙarin fargaba game da tsanantar rikicin.
Ana ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya, inda ake sa ran jami’an Lebanon da na Isra’ila za su gana a biirnin Washington cikin wannan mako domin tattauna batun tsagaita bude wutar, amma ana ganin ba a sa ran samun babban ci gaba ba, yayin da rikici ke ƙara ɗaukar zafi tsakanin ɓangarorin biyu.

0 $type={blogger}:
Post a Comment