Akalla fararen hula 20 ne, ciki har da jami’in rundunar kare fararen hula ta Lebanon, suka mutu bayan hare-haren sama da Isra’ila suka kai a wurare daban-daban na kudancin Lebanon ranar Juma’a, kamar yadda hukumomin Lebanon suka bayyana.
Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta ce mutane hudu, ciki har da mata biyu, sun mutu yayin da wasu takwas suka jikkata sakamakon harin sama da aka kai garin Toura da ke gundumar Tyre. Rahotanni sun ce jami’an ceto na ci gaba da neman wata yarinya da ta makale a karkashin baraguzan gine-gine.
Kamfanin dillancin labaran kasar Lebanon (NNA) ya kuma bayyana cewa an gano gawar wasu samari biyu bayan wani harin Isra’ila ya afkawa garin Blat da ke gundumar Marjayoun. Haka kuma an kai wasu hare-hare a yankunan Nabatieh da Bint Jbeil tare da samun karin asarar rayuka.
Hukumar Kare Fararen Hula ta Lebanon ta ce daya daga cikin jami’anta ya mutu bayan wani jirgi mara matuki na Isra’ila ya kai hari kan wata mota a hanyar Kfarchuba zuwa Kfarhamam a gundumar Hasbaya.
A cewar Ma’aikatar Lafiya, hare-haren Isra’ila a kudancin Lebanon sun kashe kusan mutane 50 cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
A gefe guda, sojojin Isra’ila sun bayar da gargadin ficewa ga mazauna wasu garuruwa da kauyuka na kudancin Lebanon da suka hada da Nmairiyeh da Tayr Felsay da Hallousiyyeh da Toura da Maarakeh.
Sojojin Isra’ila sun kuma ce wasu sojojinsu biyu sun jikkata, daya daga cikinsu da mummunan rauni, bayan wani jirgi mara matuki daga Lebanon ya kai hari arewacin yankunan da Isra’ila ke iko da su.
Hezbollah ta bayyana cewa ta kai hare-hare da dama kan sansanonin sojojin Isra’ila da motocinsu a kudancin Lebanon cikin awanni 24 da suka gabata.
Wannan sabon tashin hankali na zuwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Lebanon da Israel da aka tsawaita bayan tattaunawar da gwamnatin Donald Trump ta jagoranta a watan Afrilu.

0 $type={blogger}:
Post a Comment