EFCC Ta Ayyana Tsohuwar Minista Sadiya Farouq A Matsayin Wadda Ake Nema Ruwa A Jallo.

EFCC Ta Ayyana Tsohuwar Minista Sadiya Farouq A Matsayin Wadda Ake Nema Ruwa A Jallo.

Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC ta ayyana tsohuwar Ministar Harkokin Jin Kai da Raya Al’umma, Sadiya Umar Farouq, a matsayin wadda ake nema ruwa a jallo bisa zargin hannu a badakalar karkatar da kudaden gwamnati.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa ranar Asabar, EFCC ta ce ana neman Sadiya Farouq mai shekaru 52 da haihuwa ne kan zargin hada baki wajen aikata laifi, cin zarafin mukami da kuma karkatar da kudaden gwamnati.

Hukumar ta bayyana cewa tsohuwar ministar ‘yar asalin Jihar Zamfara ce, inda ta kuma bayar da adireshinta na karshe da ke EN 008, Okpo River, kusa da titin Agulu, Maitama, Abuja.

Sanarwar wadda mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya sanya wa hannu, ta bukaci duk wanda ke da wani bayani game da inda Farouq take da ya tuntubi ofisoshin hukumar ko kuma jami’an tsaro mafi kusa.

Sadiya Umar Farouq ta taba rike mukamin Ministar Harkokin Jin Kai, da Agajin Gaggawa da Raya Al’umma a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga shekarar 2019 zuwa 2023.

0 $type={blogger}: