Wata mummunar guguwa mai ɗauke da ruwan sama da ƙanƙara ta afkawa jihar Uttar Pradesh, jihar da ta fi yawan jama’a a ƙasar Indiya, inda ta yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 100 tare da jikkata wasu da dama.
Mahukunta sun bayyana cewa guguwar ta afku ne a ranar Laraba, inda ta lalata gidaje, ta tumbuke bishiyoyi tare da rusa rumfuna da allunan talla a yankuna da dama. Yankin da ya fi fama da ibtila’in shi ne kusa da birnin Prayagraj mai muhimmanci ga masu aikin hajjin addinin Hindu.
Jami’an agajin gaggawa sun ce akalla mutane 104 sun mutu, yayin da wasu 59 suka jikkata. Haka kuma guguwar ta lalata gidaje 87 tare da kashe dabbobi sama da 100.
Hotunan talabijin sun nuna yadda bishiyoyi da allunan talla suka fado kan motoci, yayin da iska mai ƙarfi ta dinga kwashe kayayyaki a kasuwanni da bakin hanya.
A wani bidiyo daga gundumar Bareilly, an ga yadda iska ta kwashe wani mutum daga jikin wani ƙarfen bene da yake riƙe da shi, sai dai ya tsira da raunuka.
Mahukunta sun ce mutane da dama sun rasa rayukansu ne sakamakon faɗuwar bishiyoyi da rushewar bango saboda ƙarfin guguwar.
Babban Ministan jihar Uttar Pradesh, Yogi Adityanath, ya umarci jami’ai su kai agaji cikin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa tare da raba tallafin kuɗi cikin sa’o’i 24.
Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi, shi ma ya bayar da umarnin ɗaukar matakan agaji bayan aukuwar wannan ibtila’i.
Akan samu irin waɗannan gugiyoyi a arewacin Indiya a lokacin zafi tsakanin watan Maris zuwa Yuni, kafin daminar shekara ta fara.

0 $type={blogger}:
Post a Comment