Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya isa birnin Beijing domin wata muhimmiyar ganawa da shugaban ƙasar China Xi Jinping, yayin da ƙasashen biyu ke ƙoƙarin rage tashin hankali kan harkokin kasuwanci, tsaro da batun Taiwan.
Wannan ita ce ziyarar farko da Trump ya kai China tun shekarar 2017 lokacin wa’adinsa na farko a matsayin shugaban ƙasa. Mahukuntan China sun shirya masa tarba ta musamman a babban dakin taro na Great Hall of the People, inda shugabannin biyu suka gudanar da tattaunawa tare da halartar liyafar gwamnati.
Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali kan rikicin Iran da gibin cinikayya tsakanin ƙasashen biyu da haɗin gwiwa a fannin fasahar kere-kere ta AI da kuma batun Taiwan.
Kafin barinsa Washington, Trump ya bayyana cewa yana sa ran yin “doguwar tattaunawa” da Xi musamman kan batun Iran, wadda ke sayar da yawancin man fetur ɗinta ga China duk da takunkumin Amurka.
Ma’aikatar harkokin wajen China ta ce Beijing na maraba da ziyarar, tare da nuna aniyarta ta ƙara haɗin gwiwa da Amurka tare da sarrafa sabanin da ke tsakaninsu.
Hotunan ziyarar sun nuna Trump da Xi suna duba jami’an girmamawa, ziyartar wurin tarihi na Temple of Heaven da kuma halartar liyafar cin abinci tare da manyan jami’an ƙasashen biyu.
Manyan jami’an Amurka da suka raka Trump sun haɗa da Sakataren Baitulmali Scott Bessent da Sakataren Tsaro Pete Hegseth da attajirin ɗan kasuwa Elon Musk da shugaban kamfanin Apple Tim Cook.
Masana na ganin wannan taro zai iya taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar dangantaka tsakanin Washington da Beijing a lokacin da ake fama da ƙarin gasa ta siyasa da tattalin arziki a duniya.

0 $type={blogger}:
Post a Comment