Fashewar Bom ya kashe aƙalla mutane 9 a wata kasuwa a ƙasar Pakistan.

Fashewar Bom ya kashe aƙalla mutane 9 a wata kasuwa a ƙasar Pakistan.

Akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu, yayin da kusan 30 suka jikkata, sakamakon fashewar bam a wata kasuwa mai cunkoso da ke garin Sarai Naurang a yankin Lakki Marwat na arewa maso yammacin ƙasar Pakistan, kusa da iyakar Afghanistan.

‘Yan sanda sun ce fashewar ta samo asali ne daga wata keken hawa da aka cika da bama-bamai. Daga cikin wadanda suka mutu akwai ‘yan sandan hanya biyu da kuma wata mata.

Hukumar agajin gaggawa ta Rescue 1122 ta bayyana cewa an garzaya da wadanda suka jikkata asibitoci a Bannu, inda aka ce wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

Wani jami’in lafiya ya tabbatar da cewa an karɓi marasa lafiya da dama, wasu kuma suna cikin yanayi mai tsanani.

Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin.

Wannan hari ya faru ne kwanaki kadan bayan wani hari makamancin haka a Bannu da ya kashe ‘yan sanda 21, lamarin da hukumomin Pakistan suka dora laifi kan kungiyar Tehrik-e-Taliban Pakistan (TTP).

Sai dai gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta musanta zargin, tana cewa ba ta da hannu kuma ba ta bari a kai hare-hare daga kasar ta zuwa wata kasa.

A ‘yan watannin nan, tashin hankali ya karu a arewa maso yammacin Pakistan, yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin Pakistan da Afghanistan duk da tattaunawar sulhu da aka yi a baya.

0 $type={blogger}: