Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa, (JAMB), ta amince da maki 150 a matsayin mafi ƙarancin maki da ɗalibai za su iya samu domin samun gurbin shiga jami’o’i a shekarar karatu ta 2026.
An cimma wannan matsaya ne a taron tsara manufofin shigar da ɗalibai na shekarar 2026 da aka gudanar a yau Litinin a Abuja, inda Ministan Ilimi, Tunji Alausa, tare da shugabannin jami’o’i da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.
Sabuwar ƙa’ida ta maki 150 za ta zama jagora ga jami’o’i wajen gudanar da shigar ɗalibai a zangon karatu mai zuwa.
Ana sa ran hukumar za ta fitar da ƙarin bayanai kan yadda za a gudanar da shigar ɗalibai nan gaba kadan.

0 $type={blogger}:
Post a Comment