Ƙasar Iran Ta Aiwatar da Hukuncin Kisa Kan Wanda Aka Samu da Laifin Kashe Jami'in tsaron rundunar Basij a Lokacin Rikicin watan Janairu.

Ƙasar Iran Ta Aiwatar da Hukuncin Kisa Kan Wanda Aka Samu da Laifin Kashe Jami'in tsaron rundunar Basij a Lokacin Rikicin watan Janairu.

Hukumomin shari’a na kasar Iran sun sanar da aiwatar da hukuncin kisa kan wani mutum da aka same shi da laifin kashe wani jimi'in tsaron sa-kai na rundunar Basij yayin rikicin da ya faru a watan Janairu.

Mutumin mai suna, Mehrab Abdullahzadeh, an zartar masa da hukuncin ne a safiyar Lahadi a birnin Urmia da ke arewa maso yammacin kasar, bayan Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin da aka yanke masa, tare da kammala dukkan matakan shari’a da suka dace.

Rahotannin kotu sun nuna cewa lamarin ya auku ne a lokacin tarzomar da wasu masu zanga-zanga suka tayar, inda aka rika lalata kadarorin jama’a tare da fafatawa da jami’an tsaro. Marigayin, Seyed Abbas Fatemieh, Jami'in tsaron rundunar Basij ne, kuma yana cikin tawagar da ta shiga domin dawo da doka da oda a yankin.

A cewar hukumomi, Abdullahzadeh ya tura Fatemieh har ya fadi kasa, sannan ya ci gaba da dukansa da mugun karfi, ciki har da amfani da sandar karfe, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa. Haka kuma, an ce wasu kananan yara biyu sun taka rawa a cikin harin.

Kotun Juyin Juya Halin Musulunci da ke Urmia ta same shi da laifin “lalata kasa” (corruption on earth), wanda babban laifi ne a dokar Iran da ke iya janyo hukuncin kisa. Daga bisani, Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin kafin aiwatar da shi.

Wannan lamari na daga cikin jerin matakan shari’a da hukumomin Iran ke dauka kan wadanda ake zargi da hannu a tashe-tashen hankula da suka biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar a sassan kasar.

0 $type={blogger}: