Ambaliyar Ruwa Da Zaftarewar Kasa Sun Hallaka Mutane 10 A China

Ambaliyar Ruwa Da Zaftarewar Kasa Sun Hallaka Mutane 10 A China

Akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu bayan mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya da zaftarewar kasa a wasu sassan kudanci da tsakiyar ƙasar China.

Hukumomin kasar sun bayyana cewa tsarin guguwar ruwan saman ya mamaye fiye da kilomita 1,000, kuma yanzu ya shiga mataki mafi hadari, lamarin da ya sa aka fara daukar matakan gaggawa a larduna da dama.

Hukumar kula da yanayi ta kasar China ta ce har yanzu ana ci gaba da gargadin hadarin ruwan sama mai karfi da guguwa a ranar Talata yayin da jami’an ceto ke gudanar da ayyuka a yankunan da abin ya shafa.

Gwamnatin kasar ta ayyana matakin gaggawa na ambaliya a lardunan Hunan da Guangxi, yayin da ake ci gaba da irin wannan mataki a Hubei da Guizhou da Chongqing.

Kafafen yada labaran gwamnati sun ruwaito cewa mutane shida sun mutu a Guangxi bayan wata motar daukar kaya dauke da mutane 15 ta fada cikin kogin da ya cika da ruwa sakamakon mamakon ruwan sama.

A lardin Hubei kuwa, mutane uku sun mutu bayan ambaliyar ruwa ta afkawa wani kauye da ke kasa da tudu, yayin da aka sake samun mutum daya da ya mutu a kudancin Hunan.

Bidiyoyi da suka yadu a shafukan sada zumunta na kasar sun nuna tituna sun nutse cikin ruwa a birnin Jingzhou, inda aka ga motoci kusan sun nutse gaba daya yayin da mazauna yankin ke tafiya cikin ruwa mai zurfi.

Hukumomi sun dakatar da zirga-zirgar ababen hawa, tare da rufe makarantu da wuraren kasuwanci a wasu yankunan da abin ya shafa, yayin da ake kwashe jama’a daga wuraren da ke cikin hadari.

Masana yanayi sun danganta lamarin da haduwar iska mai dauke da danshi daga Tekun Bengal da Tekun Kudancin China da kuma Tekun Pacific, wanda ya kara tsananta ruwan saman.

Masana sun kuma gargadi cewa ana sa ran mummunar guguwar za ta ci gaba da matsawa gabas da kudu cikin kwanaki masu zuwa, tare da yiwuwar karin mamakon ruwan sama a yankin kogin Yangtze.

0 $type={blogger}: