Zanga-zangar ƙarin farashin mai a kenya ta yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu, tare da jikkata mutune fiye da 30.

Zanga-zangar ƙarin farashin mai a kenya ta yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu, tare da jikkata mutune fiye da 30.

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu yayin da fiye da 30 suka jikkata a zanga-zangar da ta barke a fadin ƙasar Kenya sakamakon karin farashin man fetur.

Rahotanni sun bayyana cewa zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali a wasu manyan birane, inda aka samu arangama tsakanin masu Zanga-zangar da jami’an tsaro.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Kipchumba Murkomen, ya ce an kama akalla mutane 348 a ranar Litinin yayin rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar.

A babban birnin ƙasar, Nairobi, ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar da suka toshe hanyoyi tare da kona tayoyi a tituna.

Zanga-zangar ta kuma shafi birnin Mombasa, inda harkokin sufuri suka tsaya cak, lamarin da ya tilasta jama’a da dama yin tafiya mai nisa domin zuwa aiki da makarantu.

Kungiyoyin sufuri sun bukaci gwamnati ta janye karin farashin mai da ya kai sama da kashi 23 cikin 100, wanda ya biyo bayan wani karin farashi da aka yi a watan da ya gabata.

Gwamnatin Kenya ta kare matakin, tana mai cewa tashin farashin man fetur din ya samo asali ne daga rikicin kasuwannin mai na duniya, musamman tasirin rikice-rikicen da suka shafi Iran da mashigin jiragen ruwa na Hormuz.

Sai dai ‘yan adawa, ciki har da Rigathi Gachagua, sun zargi gwamnati da cin gajiyar lamarin, zargin da gwamnati ta musanta.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun yi Allah wadai da amfani da karfi kan masu zanga-zanga, tare da kira da a gudanar da cikakken bincike kan mutanen da suka rasa rayukansu.

A ‘yan shekarun nan, Kenya na ci gaba da fuskantar zanga-zanga da dama da suka shafi matsalolin tattalin arziki da cin hanci da rashawa, da tsadar rayuwa.

0 $type={blogger}: