‘Yan Ta’adda Sun Sake Kai Hari a jihar Kwara, Inda suka Kashe Jami'an tsaron Gandun daji guda biyar, ciki har da wani kwamanda.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne a garin Nuku da ke ƙaramar hukumar Kaiama, inda ‘yan bindigar suka kai farmaki da sanyin safiya, suka bude wuta kan jami’an tsaron gandun daji da mazauna yankin.
An bayyana cewa masu tsaron gandun dajin sun yi ƙoƙarin mayar da martani ta hanyar fafatawa da maharan, amma daga ƙarshe an rinjaye su, lamarin da ya kai ga mutuwar biyar daga cikinsu. Haka kuma, an lalata dukiyoyi da dama, ciki har da babura da gine-gine, yayin da aka kuma kona motocin sintiri na ‘yan sanda.
Harin ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba, inda da dama daga cikin mazauna suka tsere daga gidajensu domin neman tsira.
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi Allah-wadai da wannan kisan, yana mai bayyana wadanda suka mutu a matsayin jarumai da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare al’umma. Ya kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin ƙarfafa tsaro da kuma bin sawun wadanda suka kai harin.
Jami’an tsaro sun ce sun fara gudanar da bincike da kuma shirye-shiryen farautar ‘yan ta’addan domin hana sake faruwar irin wannan hari.
Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ƙaruwa a wasu sassan Jihar Kwara, musamman a yankin Kaiama, inda ake fama da hare-haren ‘yan ta’adda a ‘yan kwanakin nan.

0 Comments:
Post a Comment