An haifi Ebrahim Ra'isi ne a shekaran ranar 14 ga watan Disamban shekara 1960 a birnin Mashad mai tarihi ga mabiya Shi'an Kasar ta Iran.
Raisi ya kasance wanda ake yi ma kallon mai tsatstsauran ra'ayin rikau kuma mai gwagwarmaya.
ya kwashe shekaru yana aikin a ma'aikatar shari'ar Kasar inda ya taba Zama mataimakin Mai shigar da Kara na kasar kafin daga bisani ya Zama babban mai shigar da Kara na gwamnatin Iran din daga shekarun 2014-2016.
An kuma zabe Shi a matsayin babban Mai Alkalin alkalen Kasar daga shekaran 2019- 2021 kuma ya kasance mamba a majalisar kwararru ta Iran inda yake wakiltan lardin Khorosan.
An zabe Shi a matsayin Shugaban Kasar ta irin a shekar 2021 inda ya gaji Hassan Rouhani wanda ya kwashe shekaru takwas yana Kan karagar mulki.
Ya rasu a hadarin jirgin sama a lokacin da yake dawowa daga wajen kaddamar da bude madatsan ruwa na Qiz Qalasi and Khoda Afarin dake kan iyakar kasar iran da Azerbaijan.
Ya rasu ya bar 'ya'ya 2 wanda ya haifa da matarsa wacce ya aura a shekaran 1983, Jamileh Alamolhoda, 'yar babban malamin nan, Sayyid Ahmad Alamolhoda wanda shine limanin Juma'a na babban masallacin Mashad mai tarihi a iran kuma wakili a majalisar kwararru ta Iran.
Article Translation in English Language.
Ebrahim Ra'isi was born on the 14th day of December 1960 in Mashad, a historical city for the followers of Shi'a in Iran.
Raisi was seen as a radical and militant.
He spent years working in the Ministry of Justice where he once became the Deputy Prosecutor of the country before finally becoming the Chief Prosecutor of the Iranian government from 2014-2016.
He was also elected as the Chief Judge of the country from 2019-2021 and was a member of the Council of Experts of Iran where he represented Khorosan province. He was elected as the President of the country in 2021 where he succeeded Hassan Rouhani who has been in power for eight years.
He died in a plane crash when he was returning from the inauguration of the Qiz Qalasi and Khoda Afarin dams on the border between Iran and Azerbaijan.
He died and left behind 2 children who he had with his wife whom he married in 1983, Jamileh Alamolhoda, the daughter of the great teacher, Sayyid Ahmad Alamolhoda who is the Friday imam of the historic Mashad Mosque in Iran and a representative in the Council of Experts of Iran.
0 Comments:
Post a Comment