Kotu ta umurci EFCC ta cigaba da tsare tsohon Ministan shari'ar Najeriya, Abubukar Malami

Kotu ta umurci EFCC ta cigaba da tsare tsohon Ministan shari'ar Najeriya, Abubukar Malami

Hukumar EFCC ta cigaba da tsare tsohon ministan shari'a, Malami yayin da Kotu ta ki amincewa ta bayar da belinsa.

Wata babbar kotu da ke zamanta a babban birni tarayya Abuja, ta yi watsi da bukatar neman belin tsohon babban Lauyan kasar nan kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, na neman a sake shi daga hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Mai shari’a Babangida Hassan ya ce ba zai iya bayar da belinsa ba saboda kotun koli ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare tsohon Ministan shari'ar domin ci gaba da bincike.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Malami, jigo a jam’iyyar adawa, kuma mai neman tsayawa takarar gwamna a jihar Kebbi, ya kasance a hannun hukumar EFCC tun a makon jiya a kan zargin karkatar da kudaden gwamnati.

Malami, wanda ya nemi belin ta hannun lauyansa, Sulaiman Hassan, babban lauyan Najeriya, inda ya bayyana cewa tsare shi da Hukumar ke yi, ya sabawa doka.

Sai dai lauyan EFCC, Jibrin Okutepa, wanda kuma babban lauya ne a Najeriya, ya gabatar da cewa hukumar EFCC na tsare da tsohon ministan ne ta hanyar bayar da umarnin ci gaba da tsare shi da aka samu daga wata babbar kotun tarayya dake Abuja wanda mai shari’a S.C Oriji ya bayar.

Hakazalika ya kuma tabbatar da cewa EFCC hukuma ce mai bin doka da oda, Don haka ba za ta tsare wanda ake tuhuma har ya wuce lokacin da doka ta tanada ba, sai da umarnin kotu.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Hassan, yayin da yake ambato sashe na 35 na kundin tsarin mulkin kasar, ya ce “tunda akwai wani tanadi a hukumar kula da shari’ar laifuka ta ACJA, na tsare Malami bisa doka da oda ta hanyar Remand Order na kotu, ba zata saba wa umurnin kotun ba.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: