Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya sun ziyarci Kungiyoyin Addinin musulunci da na Kirista domin sake gina Alakar zaman lafiya a tsakanin Addinan biyu

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya sun ziyarci Kungiyoyin Addinin musulunci da na Kirista domin sake gina Alakar zaman lafiya a tsakanin Addinan biyu.

Shugabannin Arewa da suka hada da tsohon kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF), Dr Hakeem Baba Ahmed; da tsohon babban sakataren hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Farfesa Yusuf Usman; sun ziyarci hedikwatar kungiyar Kiristocin Arewacin Najeriya (CAN) 19 da kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a wani shirin karfafa dangantaka tsakanin Musulmi da Kirista a Arewacin Najeriya.

Dakta Hakeem, wanda ya jagoranci tawagar karkashin wata sabuwar kungiya da aka kafa mai suna Northern Reconciliation Group (NRG) zuwa ofisoshin kungiyoyin biyu a ranar Talata, ya ce lokaci ya yi da ya kamata Musulmi da Kirista su taru domin a zauna lafiya da juna, musamman ‘yan Arewa.

Ya bayyana cewa kungiyar ta hada da kiristoci da musulmi wadanda ’yan arewa ne kuma suna da imani daya cewa Allah ya halicce su ne a matsayin mutane daya duk da sabanin da ke tsakaninsu.

Dokta Hakeem ya ce sun yanke shawarar haduwa ne domin samar da zaman lafiya da hadin kai da sulhu a yankin saboda tuni yankin ya dandani kudansa saboda rikice-rikice da dama da aka fuskanta a yankin tsawon shekaru da dama.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar CAN na jihohin Arewa 19, Reverend Joseph John Hayab, ya ce “Za mu shaida wa duniya cewa, duk da cewa an yi ta fama da rashin fahimta a Arewacin Najeriya, wata sabuwar murya ta taso, Saboda haka ya isa’, kuma za mu warware matsalolin mu.” 

Hakazalika, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, babban sakataren JNI, ya ce idan mutane suka taru don magance wata matsala, taimakon Allah zai zo kuma abubuwa za su yi kyau.

"Bari mu nuna wa wadanda ke wurin cewa muna da karfi kuma a shirye muke kuma za mu iya yin hakan, kuma kuna da goyon bayanmu."

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: