Farashin Shanu ya yi tashin gwauron zabi inda har ya zarce kudin wasu kananan motoci a Najeriya.

Farashin Shanu ya yi tashin gwauron zabi inda har ya zarce kudin wasu kananan motoci a Najeriya.

Masu sayar da nama a Najeriya sun bayyana damuwa kan yadda farashin shanu ke ci gaba da tashi sosai, har ya kai wasu shanu ana sayar da su a kusan ₦2.5 miliyan, abin da ya sa wasu ke cewa farashin shanun ya fi na wasu motoci tsada a halin yanzu.

Masu kasuwancin dabbobi sun ce wannan tashin farashi yana kawo musu babbar matsala wajen gudanar da kasuwancinsu na yau da kullum.

An baiyana dalilan tashin farashin shanun da Matsalar tsaro a yankunan da ake kiwon shanun da kuma Karin farashin sufuri da jigilar dabbobi da Karancin ciyawa da abincin shanu sakamakon sauyin yanayi.
Wanda hakan ya jawo Karin farashin shanun a kasuwannin dabbobin.

Masu kasuwancin dabbobin sun bayyana cewa a yanzu, farashin saniya guda ya kai matakin da ya fi na wasu kananan motoci, abin da ke nuna irin tsananin tashin farashin da ake fuskanta a kasuwar dabbobi a Najeriya.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: