'Yan bindiga sun Kai Hari a Unguwar Sabon‑Titi a kan hanyar Katari zuwa Hayin Dam a ƙaramar hukumar Kachia na Jihar Kaduna Inda suka sace mutane 10 a daren ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu, 2026.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa, maharan da suka zo da yawa da makamai masu karfi sun kutsa cikin unguwar ne da misalin ƙarfe 9:32 na daren ranar Alhamis, inda suka yi awon gaba da mutum bakwai daga cikin iyali ɗaya, kafin daga bisani su nufi gidan makwabta su sace wasu karin mutane uku.
An bayyana sunayen waɗanda aka sace kamar haka:
Jummai Amos, Barnabas Amos, Iko Amos, Baby Amos, Eunice Amos, Eshiwan Amos, Godwin Amos daga cikin iyalin farko;
Sannan Bagudu Damisa, Evelyn Damisa, Alfred Iriyo daga gidan makwabta.
Wani mazaunin yankin, Markus Yakubu, ya ce maharan sun kewaye gidan da farko ba tare da harbi ba, watakila saboda kusancin wurin da gidan Shugaban ‘Yan Sandan Ƙaramar Hukuma (DPO) yake; amma daga baya an ji harbe‑harbe bayan sun bar unguwar tare da waɗanda aka sace.
Shugaban al’umma wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce duk ƙoƙarin da ya yi na tuntuɓar jami’an tsaro a lokacin lamarin ya gagara. A halin yanzu, jami’an tsaro suna gudanar da bincike a cikin dazuzzuka don ganin an samo wadanda aka sace, yayin da ƙungiyar ‘yan sanda ta Kaduna ba ta fitar da wani bayani kai tsaye ba tukuna.

0 Comments:
Post a Comment