Rahotanni daga kafar yada labarai ta Press TV sun bayyana cewa wasu dakarun Chechen da ke karkashin Rasha sun nuna shirin su na tura sojoji zuwa ƙasar Iran, idan har Amurka ta kaddamar da hari ta ƙasa a kan ƙasar.
A cewar rahoton, an bayyana cewa waɗannan dakarun suna cikin shirin ko ta kwana domin taimakawa Iran idan rikicin ya rikide zuwa cikakken yaƙi ta ƙasa. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke ci gaba da ƙaruwa a yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da hadin gwiwar Amurka da Israi'la.
0 Comments:
Post a Comment