Duniya Na Mamakin Ikon Iran Bayan ta Harba Makamai Masu Linzami Zuwa sansanin Sojin Amurka da Birtaniya a Tekun Indiya.

Duniya Na Mamakin Ikon Iran Bayan ta Harba Makamai Masu Linzami Zuwa sansanin Sojin Amurka da Birtaniya

Rahotanni na ci gaba da jawo hankalin duniya game da rahotan dake cewa ƙasar Iran ta harba makamai masu linzami zuwa sansanin Sojin Amurka da Birtaniya dake yankin Tekun Indiya, abin da ke nuna ƙara ƙarfin sojinta a fannin hare-haren nesa.

Kamfanin dillancin labarai na cikin gida, Mehr News Agency, ya ruwaito cewa Iran ta harba makamai masu linzami guda biyu zuwa sansanin sojojin haɗin gwiwa na Amurka da Birtaniya da ke Diego Garcia a Tekun Indiya.

Sai dai a baya, jaridar The Wall Street Journal ta bayyana cewa makaman masu cin matsakaicin zango da aka harba zuwa sansanin ba su yi wani gagarumin lahani ba.

Duk da haka, rahoton Mehr ya bayyana harin a matsayin wani muhimmin mataki da ke nuna cewa Iran na da ƙarfin kai hare-hare zuwa wurare masu nisa, har ma zuwa wuraren da abokan gabarta ba su zata ba.

Masu sa ido na ganin cewa irin wannan ci gaba na iya ƙara ɗaga hankulan ƙasashen duniya, musamman dangane da tsaro da daidaiton ƙarfi a yankin.

News Translation in English Language.

World Reacts as Iran Allegedly Fires Missiles Toward US-UK Military Base.

Global attention is being drawn to reports that Iran has launched missiles toward a joint United States–United Kingdom military base in the Indian Ocean, highlighting what analysts see as a growing long-range strike capability.

According to Iran’s semi-official Mehr News Agency, two missiles were fired toward the joint military facility operated by the United States and the United Kingdom at Diego Garcia in the Indian Ocean.

However, earlier reporting by The Wall Street Journal indicated that the medium-range missiles did not cause any significant damage to the base.

Despite this, Mehr described the strike as a significant step demonstrating Iran’s ability to target distant locations, including areas its adversaries may not anticipate.

Observers warn that such developments could heighten global tensions, particularly concerning security and the balance of power in the region.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: