Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ne zai Jagoranci Hawan Sallah na bana - Gwamnatin Kano.

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ne zai Jagoranci Hawan Sallah na bana - Gwamnatin Kano.

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zai jagoranci Hawan Sallah (Durbar) na Eid-el-Fitr na bana, yayin da ta ɗauki tsauraran matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa ta samu bayanan sirri da ke nuna yiwuwar wasu su yi ƙoƙarin tada tarzoma a lokacin bukukuwan Sallah.

Gwamnatin ta jaddada cewa duk da muhimmancin kiyaye al’adun gargajiya irin na Durbar, ba za ta lamunci duk wani abu da zai iya kawo barazana ga tsaro, rayuka da dukiyoyin jama’a ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa Sarkin zai fara Hawan Idi daga filin sallar Idi na Kofar Mata, inda zai bi hanyoyin da aka tsara zuwa wasu sassa na birnin kafin komawa fadar sarki.

Sai dai domin ƙarfafa tsaro, gwamnatin ta sanar da yin wasu sauye-sauye a shirye-shiryen Hawan Sallah. Hawan Nasarawa za a gudanar da shi ba tare da hawan doki ba, yayin da aka dakatar da wasu daga cikin hawaye kamar Hawan Daushe, Hawan Fanisau da Hawan Dorayi zuwa wani lokaci.

Haka kuma, an umarci jami’an tsaro su ƙara kaimi wajen sa ido tare da tabbatar da tsaron jama’a kafin, lokacin da kuma bayan gudanar da bukukuwan Sallah.

A ƙarshe, gwamnatin ta yi kira ga al’ummar jihar da su kasance masu bin doka da oda, su guji yada jita-jita, tare da ba jami’an tsaro haɗin kai domin tabbatar da an gudanar da bukukuwan cikin lumana.

News Translation in English Language.

Sanusi II to Lead Eid Durbar as Kano Tightens Security.

The Kano State Government has announced that the Emir of Kano, Muhammadu Sanusi II, will lead this year’s Eid-el-Fitr Durbar, as authorities intensify security measures to ensure a peaceful celebration.

In a statement issued by the Commissioner for Information and Internal Affairs, Ibrahim Waiya, the government disclosed that intelligence reports indicated possible attempts by some individuals to incite unrest during the Sallah festivities.

The government emphasized that while it remains committed to preserving Kano’s rich cultural heritage, including the traditional Durbar, it will not compromise on the safety of lives and property.

According to the statement, the Emir will commence the Eid procession from the Kofar Mata Eid ground, proceeding along designated routes across the city before returning to the palace.

However, as part of enhanced security arrangements, the government announced adjustments to some Durbar activities. The Hawan Nasarawa will be conducted without horse riding, while events such as Hawan Daushe, Hawan Fanisau, and Hawan Dorayi have been suspended until further notice.

Security agencies have also been directed to heighten surveillance and ensure strict enforcement of law and order before, during, and after the celebrations.

The government called on residents to remain law-abiding, avoid spreading misinformation, and cooperate with security agencies to guarantee a peaceful and successful Sallah celebration.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: